Saurari premier Radio
31.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDole ne Sule Lamido da 'ya'yansa su amsa tuhumar EFCC-Kotu

Dole ne Sule Lamido da ‘ya’yansa su amsa tuhumar EFCC-Kotu

Date:

Mukhtar Yahya Usman

 

Hukumar EFCC ta ce tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido zai fara shigar da bahasin kariya a tuhumar halasta kudin haram kimanin naira miliyan 712 daga ranar 8 zuwa 11 ga watan Nuwamban 2022.

 

Hakan na zuwa ne bayan Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta yi watsi da bukatar da tsohon gwamnan ya shigar yana neman ta kori karar da hukumar EFCC ke yi masa game da wawure miliyoyin.

 

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta gurfanar da Sule Lamido da ‘ya’yansa biyu, Aminu Sule Lamido da Mustapha Sule Lamido da wani Aminu Wada Abubakar da Bamaina Holdings Ltd da kuma Kamfanin Speeds International Ltd bisa zargin damfarar jihar Jigawa.

Ta ce ta gurfanar da tsohon gwamnan ne kan tuhuma 37 da aka yi wa gyara wadda ta danganci tozarta mukami da kuma halarta kudin haram kimanin naira miliyan 712.

 

Hukumar ta zargi Sule Lamido ne da tozarta mukaminsa na gwamna a tsakanin shekarar 2007 da 2015 ta hanyar ba da kwangiloli ga kamfanonin da yake da alaka da su, inda ya rika amfani da ‘ya’yansa wajen yin rufa-rufa.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories