24.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiMuna so a hukunta dan uwanmu da ya kashe Ummita-‘Yan China mazauna...

Muna so a hukunta dan uwanmu da ya kashe Ummita-‘Yan China mazauna Kano

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Mukhtar Yahya Usman

 

Al’ummar China mazauna Kano sun bukaci a hukunta dan kasarsu da ake zargi da kisan wata mata ‘yar Kano mai suna Ummukulsun Buhari  a unguwar Jambulo.

 

Wannan na kunshe cikin wata samarsa da Wakilin Mutanen China a Kano Mike Zhang ya fitar ranar Litinin a Kano.

 

Sanarwar ta yi Allah wadai da kisan matashiyar, kuma ta bukaci a hukunta shi dai-dai da abinda ya aikata.

 

Haka zalika ta bukaci mahukunta su gudanar da binciken kwakwafi kan lamari daga dukkanin bangarorin jami’an tsaro.

 

Sanarwar ta ce al’ummar China a Kano na bin dukkanin dokokin kasa kuma suna bin duk dokar da aka gindaya musu.

 

Su kuma nuna jin dadinsu kan irin damar da aka basu suke zaune a Kano ba tare da takuraba.

 

Al’ummar ta kuma mika sakon ta’aziyyarta ga iyalai da dangin mamaciyar inda suka roki Allah ya gafarta mata.

 

Latest stories