Saurari premier Radio
38.9 C
Kano
Thursday, April 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiBashin Najeriya ya karu zuwa tiriliyan 42-DMO

Bashin Najeriya ya karu zuwa tiriliyan 42-DMO

Date:

Mukhtar Yahya Usman

 

Ofishinda ke kula da basuka na kasa DMO ya ce bashin da ake bin Najeriya ya karu zuwa Naira tiriliyan 42.

 

A cewar ofishin daga Maris zuwa Yunin 2022 kasar nan ta ciyo karin bashin Dala biliyan uku, wanda ya kara adadin bashinta zuwa Dala biliyan 103.31 daga Dala biliyan 100.

Hakan na nufin idan aka raba wa ’yan Najeriya mutum miliyan 200 bashin, kowannensu zai biya Naira 210,000.

Idan aka kwatanta da kasafin Naira tiriliyan 19.97 na shekarar 2023 da Shugaba Buhari zai gabatar a watan Oktoba, bashin ya ninka kasafin sau biyu da doriya.

 

Sanarwar da ofishin ya fitar ta ce “Basukan da ake bin mu sun karu ne saboda rancen da Gwamnatin Tarayya ta karba domin cike gibin da aka samu a kasafin 2022 da kuma basukan da gwamnatocin jihohi da Birnin Tarayya suka ciyo,” a cikin wata ukun.

 

DMO ya bayyana cewa a tsawon watan ukun basukan cikin gida sun karu zuwa Naira tiriliyan N26.23 (Dala biliyan 63.24); amma ba a samu kari na kasashen waje ba daga Naira tiriliyan 16.61 (Dala biliyan 39.96).

 

A karshen watan Maris na 2022, Naira tiriliyan 24.98 (Dala biliyan 60.1 ne bashin da ake bin gwamnatocin a cikin gida.

 

DMO ta bayyana cewa fiye da rabin basukan da gwamnatocin suka ciyo an karbe su ne ta hanyar jingina ko ayyukan hadin gwiwa.

 

“Sama da kashi 58 na basukan kasashen wajen kan karbo su ne ta hanyar jingina, Lamuni ko domin aiwatar da ayyukan hadin gwiwa.

 

“An karbo su ne daga masu ba da rance na kasa da kasa irin su Bankin Duniya, Asusun Lamuni na Kasa da Kasa, Bankin Afrexim, Bankin Raya Kasashen Afrika, da kasashen Jamus, China, Japan, India da Faransa.

 

Ta ci gaba da cewa har yanzu yawan basukan na kashi 23.06 cikin 100 bai wuce misali ba idan aka kwatanta da yawan kayayyakin da ake samarwa a cikin kasar.

 

Ta bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta dukufa wajen bullo da sabbin hanyoyin samun kudaden shiga da kuma rage basukan da ake bin ta.

Latest stories

Hukumar EFCC ta musalta zargin da ake mata na fara bincikar tsohon Gwamnan kogi.

Shugaban hukumar EFCC mai hukunta masu yiwa tattalin arziki...

Majalisar dokokin Kano ta nemi a dakatar da KEDCO kan yanke wuta.

Majalisar Dokokin jihar Kano ta bukaci gwamnatin jihar data...

Related stories

Hukumar EFCC ta musalta zargin da ake mata na fara bincikar tsohon Gwamnan kogi.

Shugaban hukumar EFCC mai hukunta masu yiwa tattalin arziki...

Majalisar dokokin Kano ta nemi a dakatar da KEDCO kan yanke wuta.

Majalisar Dokokin jihar Kano ta bukaci gwamnatin jihar data...