Saurari premier Radio
31.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAn kama mushen dabbobi a mayankar Unguwa Uku

An kama mushen dabbobi a mayankar Unguwa Uku

Date:

Mukhtar Yahya Usman

 

Hukumar kare hakkin masu sayan Kayayyaki ta Jihar Kano (KSCPC) ta ce ta gano tare da kama wasu matattun dabbobi a mayankar Unguwa Uku Yan Awaki da ke karamar hukumar Tarauni.

 

Mukaddashin Manajan Daraktan hukumar, Baffa Babba-Dan Agundi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Musbahu Yakasai ya fitar ranar Litinin a Kano.

 

Babba-Dan Agundi, wanda babban mataimaki na musamman ga gwamnan Kano  kan harkokin tabbatar da ingancin kayayyakin masarufi, Alhaji Salisu Muhammad, ya wakilta, ya ce hukumar ta samu rahoton matattun dabbobin ne da misalin karfe 6:00 na safiyar ranar Litinin.

 

“Nan take tawagarmu ta dunguma zuwa can ta kuma dauki mataki tare da kame dabbobin a kokarin da muke na kare mutanen Kano daga amfani da kayayyakin da ba su da inganci.”

 

Ya yi nuni da cewa hukumar ta gayyaci wani Likitan Dabbobi domin ya gwada dabbobin ko sun dace dan Adam ya ci namansu tare da tabbatar da ko da gaske yawancinsu sun mutu kafin a yanka su.

 

“Za a hukunta wadanda ake zargi da laifin dai dai da abinda suka aikata.”

 

Babba-Dan’agundi ya yi kira ga mahautan dake mayankar Unguwa Uku ‘Yan Awaki da ma Kano baki daya, musamman masu yin ha’inci da su daina irin wannan aiki ko kuma su fuskanci fishin doka.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories