Saurari premier Radio
21.8 C
Kano
Saturday, March 2, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiBa za mu yi karin man fetur a Disamba ba-NNPC

Ba za mu yi karin man fetur a Disamba ba-NNPC

Date:

Mukhtar Yahya Usman

 

Kamfanin man fetur na kasa (NNPC) ya ce kasar nan ba za ta fuskanci karancin man fetur a watan Disamba da kuma bayanta ba, la’akari da tanadin isasshen albarkatun man feturin da Kamfanin ya yi.

 

Babban jami’in kula da harkokin kudi na kamfanin Umar Ajia ne ya bayyana hakan a lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin wucin gadi na majalisar wakilai kan tsarin tallafin man fetur a Najeriya.

 

Ajia ya bayyana cewa kamfanin ya samar da isassun matakan dakile matsalar karancin man fetur a kasar, ko da bayan babban zaben 2023.

 

Shugaban Kwamitin kulada sarrafa albarkatun man fetir Ibrahim Al-Mustapha daga jihar Sokoto ya ce akwai bukatar a kara yin nazari a kan farashin man fetur a Najeriya, daidai da farashin mai a duniya.

 

Al-Mustapha ya ce ana sayar da man fetur a kan Naira 536 a kowace lita a jamhuriyar Nijar, sai kuma Naira 577 a Mali da kuma Naira 389 a Jamhuriyar Benin.

 

Ajia ya ce man fetur da ake baiwa ‘yan Najeriya tallafin man fetur ana jigilar su zuwa kasashe makwabta.

 

Ya ce a sakamakon dagulewar al’amuran iyakokin, hakan kan sanya zirarewar tallafin man fetur da ‘yan Najeriya za su sha da sauran kasashe makwabta.

 

“Idan kuna da Naira miliyan 5, za ku iya tsallaka kan iyaka da manyan motoci da man fetur, muna da iyaka; eh muna da kwastam amma duk tamkar rariya,” inji shi.

 

Kwamitin ya shiga wani zaman sirri don kara tattaunawa kan lamarin.

Latest stories

CBN Ya Kwace Lasisin Yan Canji Sama da Dubu Hudu A Faɗin Nijeriya

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da soke lasisin...

Dangote ya bayar da shawarar mayar da kasuwar waya ta Farm Center zuwa cibiyar fasaha

Fitaccen attajirin nan, Alhaji Aliko Dangote, ya shawarci jami'ar...

Related stories

CBN Ya Kwace Lasisin Yan Canji Sama da Dubu Hudu A Faɗin Nijeriya

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da soke lasisin...

Dangote ya bayar da shawarar mayar da kasuwar waya ta Farm Center zuwa cibiyar fasaha

Fitaccen attajirin nan, Alhaji Aliko Dangote, ya shawarci jami'ar...