Saurari premier Radio
24.9 C
Kano
Thursday, April 11, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiYadda wata Mata ta saci yara 9 a Danbatta

Yadda wata Mata ta saci yara 9 a Danbatta

Date:

Mukhtar Yahya Usman

 

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta ce ta kama wata mata da ake zargi da sato yara 9 daga garin Danbatta.

 

Ana dai zargin matar ne da satar yaran da nufin sayar da su a jihar Ogun.

 

Kakakin Rundunar yan sandan jihar Kaduna DSP Muhammad Jalige ne ya bayyana Hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.

 

Jalige ya ce yaran wadanda shekarunsu basu haura 10 zuwa shabiyar ba matar ta nufi garin Ijebu Ode ta jihar Ogun.

 

Ya ce an kama matar ne a shingen bincike na Kurmin Mashi bayan da suka lura motar da suke ciki babu taga duk da cewa akwai mutane a cikinta.

 

“Da misalin karfe 4:00 na yammacin Lahadi ne jami’anmu suka kama motar.

 

“Matar da yaran da ta sato yan a asalin garin Dambatta ne.

 

“Ko da yake ta ce ta dauko su ne don tayata sana’ar siyar da abinci da take yi a jihar Ogun.

 

Kakakin ya ce za su ci gaba da bincike kan lamarin, kafin daukar mataki na gaba.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories