24.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiShekarau ne Dan takarar sanatan Kano ta tsakiya a ANPP-INEC

Shekarau ne Dan takarar sanatan Kano ta tsakiya a ANPP-INEC

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

 

Mukhtar Yahya Usman

 

Hukumar zabe ta kasa INEC ta bayyana sunanan Malam Ibrahim Shekarau a matsayin Dan takarar sanatan Kano ta tsakiya a jam’iyyar ANPP.

 

An dai gano sunanan Malam Shekarau din ne cikin jerin sunayen da hukumar ta fitar na karshe kan wadanda za suyi takara a jam’iyyu daban daban na kasar nan.

 

Idan za a iya tunawa a watan da ya gabata ne Malam Ibrahim Shekarau ya fice daga jam’iyyar ta ANPP inda yake takarar Sanata.

 

An dai jiyo Malam Shekarau na cewa ya fice daga jam’iyyar ne saboda rashin Adalcin da Rabiu Musa Kwankwaso ya nuna masa.

 

Hakan ce ta Sanya Dan takarar shugaban Kasa a jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya gayyace ce shi zuwa jam’iyyar PDP.

 

An ji Shekarau na cewa ya koma jam’iyyar PDP “kuma takarar Sanata a jam’iyyar ANPP a Kai kasuwa.”

 

Sai dai bayan da hukumar  INEC ta fitar da sunayen karshe na Yan takara sai aka gano sunan Shekarau dai har yanzu a jam’iyyar ANPP.

Latest stories