Saurari premier Radio
39.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiZa a gurfanar da Dan China da ya kashe Ummita a Kotu.

Za a gurfanar da Dan China da ya kashe Ummita a Kotu.

Date:

Mukhtar Yahya Usman

 

Rundunar yan sandan jihar Kano za ta gurfanar da Dan Chinan nan Ghen Quanrog gaban Kotu bisa zargin kashe Ummikulsum da aka fi Sani da Ummita.

 

Idan za a iya tunawa Mista Quanrong ya bi Ummukhulsum ne har gidan iyayenta ya caccaka mata wuka ya kasheta a ranar Juma’ar da ta gabata.

 

Ayu Laraba ne dai za a gurfanar da wanda ake tuhumar a gaban kotu, yayin da jami’an ‘yan sanda suke ci gaba da gudanar da bincike.

 

Labarin kisan matashiyar ya tayar da hankulan jama’a a jahar , yayinda har yanzu wasu ke ta mamakin yadda wannan lamari ya kasance.

 

Wadda aka hallaka ɗin abaya sun taɓa yin soyayya da Quanrong kafin ta yi aure wanda daga baya suka rabu da mijinta.

 

Wannan lamari na zuwa ƙasa da watanni biyu da yanke wa malamin makarantar boko nan Abdulmalik Tanko Muhammad da Abokinsa Hashim Isiyaku hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan sun hallaka Hanifah Abubakar Abdusslam a ƙarshen shekarar 2021

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories