Saurari premier Radio
28.9 C
Kano
Friday, May 17, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin KanoHukumar kula da asibitocin Jihar Kano ta amince da korar wasu manyan...

Hukumar kula da asibitocin Jihar Kano ta amince da korar wasu manyan jami’an lafiya sanadiyar sakaci da aiki

Date:

Hukumar kula da asibitoci ta Jihar Kano, ta amince da korar manyan jami’an lafiya na babban asibitin Imam Wali da Abubakar Imam Urology Centre da kuma na Nuhu Bamalli.

Cikin wata sanarwa da jami’ar hulda da jama’a ta hukumar Samira Sulaiman ta fitar, ta ce babban sakataren hukumar, Dr. Mansur Nagoda, ne ya tabbatar da amincewar tare da maye gurbinsu da gaggawa.

Nagoda ya kuma amince da dakatar da duk likitoci da ma’aikatan jinya da ke bakin aiki a yammaci da daren ranar Lahadin da ta gabata.

Ya ce an dauki matakin ne cikin gaggawa saboda sakaci da ma’aikatan da abin ya shafa suke yi wajen gudanar da ayyukansu ta hanyar kauracewa ayyukansu da barin marasa lafiya a hannun dalibai.

Ya kuma yi gargadin cewa hukumar ba za ta amince da sakaci da zuwa a makare ba da gujewa aiki daga duk wani ma’aikacin lafiya, in da ya kara da cewa duk wanda aka samu zai fuskanci hukunci.

Nagoda ya yi kira ga sauran asibitocin da su kara kaimi domin za a sanya ido sosai kan dukkan kayayyakin aiki domin farfado da fannin lafiya a nan Kano.

Latest stories

Kananan Hukumomi 14 A Kano Na Fuskantar Barazanar Ambaliya A Bana

Mukhtar Yahya Usman Hukumar kula da yanayı ta kasa NİMET...

Related stories

Kananan Hukumomi 14 A Kano Na Fuskantar Barazanar Ambaliya A Bana

Mukhtar Yahya Usman Hukumar kula da yanayı ta kasa NİMET...