Saurari premier Radio
33.4 C
Kano
Saturday, December 2, 2023
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDan majalisar jiha na Bebeji Ali Tiga, ya jagoranci ma'aikatan lafiya domin...

Dan majalisar jiha na Bebeji Ali Tiga, ya jagoranci ma’aikatan lafiya domin gano wata Annoba data bulla a garin Gargai.

Date:

Dan majalisar jiha na Bebeji Ali Tiga, ya jagoranci ma’aikatan lafiya domin gano wata Annoba data bulla a garin Gargai.

Dan majalisar jiha na Bebeji Ali Muhammad Tiga, ya jagoranci hukumomin lafiya na jihar Kano domin bincike kan wata cuta da aka ce ta bulla a garin Gargai dake karamar hukumar Bebeji.

Ali Muhammad Tiga, ya kai ziyarar ne a ranar Laraba.

Cutar dai tafi kama kafafun al’ummar yankin inda da zarar mutum yaji ciwo baya warkewa.

Cutar dai kan fadada a kafar mutum tare da zagwanye naman kafar wanda ta kama.

A kalla mutane fiye 25 suka kamu da wannan ciwo a garin na Gargai.

Dan majalisar Ali Muhammad Tiga, ya kuma dauki nauyin kula da masu cutar asibitin garin kafin Gano ainihin abinda ke haddasa cutar a tsakanin al’ummar garin.

Ya kuma samar da katin asibiti fiye da dubu goma ga al’ummar garin na Gargai da karamar hukumar Bebeji domin kula da marasa lafiya.

Ali Muhammad Tiga, ya kuma ce zai tabbatar da cewa an gano ainihin abinda ke haddasa cutar tare da samar musu da mafita.

 

 

Latest stories

Related stories