Saurari premier Radio
28.9 C
Kano
Friday, May 3, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiMalaman makaranta sun nemi gwamnatin Kano ta kara musu albashi

Malaman makaranta sun nemi gwamnatin Kano ta kara musu albashi

Date:

Shugaban kungiyar malaman makaranta na ƙasa reshen jihar Kano Baffa Ibrahim Garko, yayi kira ga gwamnatin Kano ta karawa malaman makaranta albashi duba da yanayin rayuwa da ake ciki.

Baffa Garko, yayi wannan kira ne a wani taro da kungiyar ta gudanar a makon nan.

Ya kara da cewa malaman makaranta sun shiga mawuyacin hali bisa kara farashin man fetur da hauhawar farashin kayayyaki.

2023: Malamai su daina yiwa ‘yan siyasa addu’a don neman kudi-Muhammadu Sanusu II

Ya kara da cewa a kungiyan ce suna kokarin fito da tsare-tsare da zasu ragewa malaman makaranta matsalolin da tashin farashin mai ya haddasa a kasar nan.

Baffa Garko ya kuma bukaci malaman Firamare da Sakandire da su kara hakuri a daidai lokacin da kungiyar ke fafutukar sama musu mafita.

Latest stories

Related stories