Saurari premier Radio
28.9 C
Kano
Friday, May 17, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnan jihar Katsina Dikko Radda zai dauki malaman makaranta 693.

Gwamnan jihar Katsina Dikko Radda zai dauki malaman makaranta 693.

Date:

Gwamnan jihar Katsina Dikko Radda zai dauki malaman makaranta 693.

Gwamnan ya baiwa kwamitin kula da daukar sabbin malaman umarnin sanya malam Part-time da malaman wucin gadi dake karkashin ma’aikatar ilimi cikin shirin daukar sabbin malaman makarantar.

Wannan na cikin sanarwar da babban maitamakawa gwamna Dikko Umaru Radda kan kafafen yada labarai na zamani Isah Miqdad ya fitar.

Gwamna Zulum Ya Tsawaita Shekarun Kammala Aikin Malamai A Jihar Borno

Tuni dai kwamitin ya fara tantance malaman wucin gadin dana sa kai dake koyarwa a makarantun sakandire daban daban na jihar.

Cikin abubuwan da malaman ke zuwa tantancewar sun hada da lambar BVN da hoto da lambar waya da shaida daga shugaban makarantar da mutum yake koyarwa.

Wannan dai na cikin manyan ayyukan da gwamna Dikko Radda ya fara aiwatarwa tun bayan rantsar dashi a matsayin gwamnan jihar Katsina.

 

 

Latest stories

Kananan Hukumomi 14 A Kano Na Fuskantar Barazanar Ambaliya A Bana

Mukhtar Yahya Usman Hukumar kula da yanayı ta kasa NİMET...

Related stories

Kananan Hukumomi 14 A Kano Na Fuskantar Barazanar Ambaliya A Bana

Mukhtar Yahya Usman Hukumar kula da yanayı ta kasa NİMET...