Saurari premier Radio
23.5 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKiwon LafiyaManoman kubewa a fadin kasar nan sun koka game da sabuwar...

Manoman kubewa a fadin kasar nan sun koka game da sabuwar cuta da ke addabar gonakinsu

Date:

Manoman kubewa a fadin kasar nan sun koka game da wata sabuwar cuta da ke addabar gonakinsu.

Manoman sun bayyana yadda cutar ta lalata kusan kashi saba’in cikin dari na kayan amfanin gonakinsu.

Cibiyar binciken kayan lambu ta kasa ta tabbatar da gano kwayar cutar yayin tattara rahotannin da ta samu daga manoman kasar nan daban-daban, musamman a jihohin Lagos, da Osun, da Ondo, da Oyo, da Ogun, da Neja, da jihar Ekiti.

Hukumar ta ce alamun cutar sun hada da wani kullutu da ke fitowa a karkashin ganyen kubewar, inda daga bisani yake nannadewa tare da sauya launi zuwa rawaya.

Cibiyar binciken kayan lambun ta shawarci manoman su yi wa gonakin kubewarsu feshin maganin kwari kowanne mako da zarar sun ga alamun cutar, tare da bayar da tabbacin dukufa wajen bincike domin samar da nagartaccen maganin da zai kashe cutar nan ta ke.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...