Saurari premier Radio
35.9 C
Kano
Sunday, May 5, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiFemi Falana zai wakilci Hukumar karbar korafi da yaki da rashawa ta...

Femi Falana zai wakilci Hukumar karbar korafi da yaki da rashawa ta jihar Kano a shari’ar bidiyon Dala

Date:

Hukumar karbar korafi da yaki da rashawa ta jihar Kano ta ce ta dauko hayar Femi Falana, babban lauyan nan mai fafutukar kare hakkin dan Adam, domin ya wakilce ta a takaddamar bidiyon dala da ake tuhumar tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da zargin karbar na goro.

Lauyan hukumar, Usman Fari, ya bayyana haka bayan fara sauraron shari’ar da kotu ta dage zuwa ranar Talatar makon gobe.

Dage zaman ya biyo bayan bukatar karin lokaci domin tattaro hujjojin kare tuhumar da ake yi wa wanda yake wakilta da lauyan Ganduje, Basil Hemba ya gabatar.

An dai sa ran ganin babban Lauya Femi Falana shi da tawagarsa a Kano da safiyar jiya Juma’a, amma Rahotanni sun ce sun gamu da cikas sakamakon rashin tasowar jirginsu daga Lagos.

Latest stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Related stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...