Saurari premier Radio
23.5 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKungiyar ma'aikatan kananan hukumomi ta kasa ta nemi gwamnatin tarayya ta karawa...

Kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi ta kasa ta nemi gwamnatin tarayya ta karawa ma’aikata albashi da kashi 300

Date:

Kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi ta kasa, ta nemi gwamnatin tarayya ta ƙarawa ma’aikata albashinsu da kimanin kashi dari uku.

Wannan dai na zuwa ne bayan janye tallafin man fetur, da ma kara farashinsa a kasar nan da ke ci gaba da janyo martani daga kungiyoyin kwadago wadanda ke hankoron ganin sun samawa mambobinsu albashin da zai iya rike su a wannan lokaci da rayuwa ta yi tsanani.

Sai dai a wannan karon a iya cewa bukatar ma’aikatan kananan hukumomin ta ci karo da bukatar uwar kungiyar kwadago ta NLC, wadda ta nemi gwamnatin tarayyar ta yi wa ma’aikata karin kashi dari biyu na albashi.

Sai dai sanarwar da shugaban kungiyar NULGE Comrade Ambali Olatunji ya fitar ta ce ta cimma matsaya ne kan abun da ta nema na karin bayan taron kolin da ta gudanar, inda ta ce shi ne ya dace da ma’aikatanta a matsayin mafi karancin albashi.

Mataimakin shugaban kungiyar ma’aikatan kananan hukumomin, Comrade Muhammad Gudaji, ya ce kofarsu a bude take domin tattaunawa da gwamnatin a kokarin samun maslaha domin tsamo jama’a daga halin da suke ciki.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...