Saurari premier Radio
21.8 C
Kano
Saturday, March 2, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin Tarayya zata dauki sabbun matakan ragewa alumma radadin cire tallafin man...

Gwamnatin Tarayya zata dauki sabbun matakan ragewa alumma radadin cire tallafin man fetur

Date:

Majalisar kula da tattalin arzikin kasa ta sanar da wasu sababbin matakai da gwamnati za ta dauka domin samawa al’umma saukin rayuwa sakammakon wahalar janye tallafin man fetur.

Majalisar ta sanar da matakan ne a karshen taron wata-wata da ta yi a karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, inda aka tattauna kan janye tallafin mai da karyewar darajar naira, da suka fi tasiri wajen jefa jama’ar kasar nan cikin mawuyacin hali.

Taron ya amince da daukar wasu matakan gaggawa domin tsamo ‘yan Nijeriya, musamman marasa galihun cikinsu,daga halin da suka shiga.

Daga ciki akwai bukatar kowacce jihar ta tsara yadda za ta samawa jama’arta sauki, ko dai ta hanyar raba tallafin kudi ko ta hanyar da ta fi dacewa.

Haka-zalika, an amince da matakin ba ma’aikatan gwamnati tallafin kudi a kan albashinsu tsawon wata shida, sannan kowacce jiha ta tabbatar ta biya ma’aikata da ‘yan fansho dukkan bashin da suke bi.

Taron ya amince da aiwatar da wani tsarin sauya makamashin man fetur da ya yi tsada yanzu zuwa wani nau’in gas da ake kira CNG a takaice wanda kasar nan ke da shi mai tarin yawa, ga kuma araha.

Latest stories

CBN Ya Kwace Lasisin Yan Canji Sama da Dubu Hudu A Faɗin Nijeriya

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da soke lasisin...

Dangote ya bayar da shawarar mayar da kasuwar waya ta Farm Center zuwa cibiyar fasaha

Fitaccen attajirin nan, Alhaji Aliko Dangote, ya shawarci jami'ar...

Related stories

CBN Ya Kwace Lasisin Yan Canji Sama da Dubu Hudu A Faɗin Nijeriya

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da soke lasisin...

Dangote ya bayar da shawarar mayar da kasuwar waya ta Farm Center zuwa cibiyar fasaha

Fitaccen attajirin nan, Alhaji Aliko Dangote, ya shawarci jami'ar...