Saurari premier Radio
40.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin Imo ta kara mafi karancin albashi zuwa dubu 40.

Gwamnatin Imo ta kara mafi karancin albashi zuwa dubu 40.

Date:

Gwamnatin Imo ta kara mafi karancin albashi zuwa dubu 40.

A kokarin ragewa ma’aikata tasirin cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya tayi gwamnatin Imo ta kara mafi karancin albashi ga ma’aikatan jihar zuwa dubu arba’in.

Yayin taron masu ruwa da tsaki a Owerri, babban birnin jihar gwamna Hope Uzodinma, ya ce gwamnatin sa zata fitar da naira biliyan biyar domin baiwa manoma bashi.

Gwamnan Zamfara ya rage ma’aikatun jihar daga 28 zuwa 16
Gwamnan ya kuma bayyana wasu hanyoyi da gwamnatin zata bi domin ragewa al’ummar jihar radadin cire tallafin.

Gwamnan ya ce yayi matukar damuwa bisa halin da al’ummar jihar suka shiga sakamakon cire tallafin wanda hakan yasa ya shi kara mafi karancin albashin da fito da sabbin tsare-tsare.

Idan za a iya tunawa a ranar 29 ga watan Mayu da ya gabata ne yayin rantsar dashi shugaba Bola Ahmad Tinubu ya sanar da cire tallafin wanda hakan ya janyo tashin farashin mai daga naira 184 kowace lita zuwa 550.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories