Saurari premier Radio
36 C
Kano
Tuesday, June 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnan Zamfara ya rage ma'aikatun jihar daga 28 zuwa 16

Gwamnan Zamfara ya rage ma’aikatun jihar daga 28 zuwa 16

Date:

Gwamna Dauda Lawal na Zamfara ya zaftare ma’aikatun jihar daga 28 zuwa 16.

A cewar mai magana da yawunsa, wanda ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa, an dauki matakin ne domin kawar da almubazzaranci.

Sabbin ma’aikatun da suka sami shiga sun hada da na noma, kasafi da tsare tsare, kimiyya da fasaha, sai ma’aikatar muhalli da ma’adanai, da ta kudi, lafiya da kuma na kasuwanci da masana’antu.

Sauran sun hada da ma’aikatar yada labarai da al’adu, shari’a, tsara birane ta kananan hukumomi, sai ma’aikatun harkokin addini, harkokin mata, ayyuka, matasa da wasanni, da kuma ma’aikatar tsaro da harkokin cikin gida.

A wani cigaban kuma, gwamnan ya tabbatar da kammala biyan ma’aikata albashin da su ke bi, har da na watan da ya shude.

Latest stories

Za’a iya shafe shekaru kafin kawo ƙarshen ƴan bindiga”- Sarkin Musulmi.

Mai Alfarma Sarkin Muslmi, Sultan Sa’ad Abubakar III, ya...

Gwamnatin Sokoto tayi martani ga mataimakin shugaban ƙasa.

Gwamnatin Sakkwato ta yi martani ga Mataimakin Shugaban Kasa...

Related stories