Saurari premier Radio
25.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin Tarayya Ta Dakatar Da Kamfanin Jiragen Sama Na Max Air.

Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar Da Kamfanin Jiragen Sama Na Max Air.

Date:

Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta kasa NCAA, ta dakatar da kamfanin jiragen sama na Max Air daga zirga-zirga nan take.

Cikin wata wasika da daraktan hukumar, Kyaftin Ibrahim Bello Dambazau ya aikewa kamfanin, ya ce an dakatar da ayyukan kamfanin saboda matsalolin da ake samu da jiragen kamfanin samfurin Boeing BB737.

Daraktan ya ce hukumar ta kafa kwamitin bincike da za su tantance ingancin jiragen saboda ba za a kyale kamfanin ya ci gaba da amfani da jiragen Boeing 737 ba har sai bayan kammala binciken.

Ya ce daga matsalolin akwai lalacewar tayar jirgin na Max Air da ya tashi daga Yola zuwa Abuja da kuma gurbatar mai da aka samu a wani jirgin irinsa da ya haddasa wutar lantarkin jirgin ta ki aiki a filin jirgin saman Yola a ranar 7 ga Mayun 2023.

Haka kuma injin wani jirgin nasu na 737 ya sami matsalar daukar zafi a ranar 11 ga Yulin 2023 a tashar jiragen saman Malam Aminu Kano, abinda ya sa jirgin ya kasa tashi.

Sai kuma saukar gaggawa da wani 737 din ya yi a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja saboda daukar zafi a mazaunin matukin jirgin a ranar 11 ga Yulin 2023.

Latest stories

Related stories