Saurari premier Radio
26.3 C
Kano
Sunday, May 5, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiZulum Ya Nada Tsohon Ministan Noma a Matsayin Sakataren Gwamnatin Jihar Borno.

Zulum Ya Nada Tsohon Ministan Noma a Matsayin Sakataren Gwamnatin Jihar Borno.

Date:

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya nada tsohon ministan noma da raya karkara, Malam Bukar Tijjani a matsayin sakataren gwamnatin jihar.

Wata sanarwa da kakakin gwamnan, Malam Isa Gusau ya fitar, ta ce Zulum ya yi la’akari da ƙwarewar da Bukar Tijjani ya nuna lokacin da ya yi minista daga Yulin 2011 zuwa Satumba 2013 da kuma mukamin da ya rike na mataimakin babban daraktan hukumar abinci da noma ta majalisar dinkin duniya FAO.

Tsohon ministan ya kuma rike shugabancin shirin samar da abinci na kasa da kuma shirin bunkasa noman rani na bankin duniya wato Fadama a Najeriya.

Sanarwar ta ce, kasancewar gwamna Zulum farfesa a fannin noman rani ya nada tsohon ministan ne a matsayin sakataren gwamnatinsa domin taimakawa wurin bunkasa noma da wadatar da jihar Borno da abinci.

Malam Bukar Tijjani mai shekaru 62 dan asalin karamar hukumar Dikwa ne amma haifaffen garin Damasak na jihar Borno, ya yi digirin farko a Amurka a 1984 sannan ya yi digirinsa na biyu a Ingila a 1989 duk a fannin noma.

Latest stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Related stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...