Saurari premier Radio
35.9 C
Kano
Saturday, May 4, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin Jihar Kano Ta Kaddamar Da Feshin Maganin Sauro A Asibitocin Jihar.

Gwamnatin Jihar Kano Ta Kaddamar Da Feshin Maganin Sauro A Asibitocin Jihar.

Date:

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana zazzabin cizon sauro a matsayin daya daga cikin cututtukan da take fatattaka a tsakanin al’umma.

Shugaban hukumar kwashe shara ta jihar Kano, Alhaji Ahmadu Haruna Zago ne ya bayyana hakan lokacin da yake kaddamar da aikin feshin maganin sauro a asibitin Gwagwarwa da ke karamar hukumar Nassarawa.

Yace sun samu rahotannin cewa an shafe kusan shekaru 8 ba’a yi aikin feshin maganin ba a asibitoci da unguwannin Kano, don haka ya ce akwai bukatar al’umma su ci gaba da karfafa yunkurin gwamnati wajen inganta rayuwarsu.

Wasu daga cikin marasa lafiyar da ke asibitin sun ce da yawan majinyata a asibitocin gwamnati a yanzu suna kwasar cutar cizon sauro ne a asibitocin maimaikon sama musu lafiya.

Asibitocin da aka fara gudanar da aikin feshin maganin sauron Larabar nan, sun hada da na Sir Sunusi da na Gwagwarwa sai Kuma na Waziri Gidado dake unguwar Bachirawa.

Latest stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Related stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...