Saurari premier Radio
35.9 C
Kano
Saturday, May 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnan Kano ya kalubalanci tsarin Tinubu na rabawa yan kasa tallafin dubu...

Gwamnan Kano ya kalubalanci tsarin Tinubu na rabawa yan kasa tallafin dubu 8000

Date:

Gwamnatin jihar Kano ta ce akwai matsala dangane da rabon naira milyan dubu dari biyar da shugaba Ahmad Bola Tinubu ya ce za a ba ‘yan Nijeriya domin rage radadin cire tallafin mai.

Da ya ke jawabi yayin taron da wasu wakilan kungiyar gama kai ta jiha, gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce tsarin da aka bi na fitar da kudin daga bankin masana’antu domin taimakawa ci gaban kananan masa’antu a shioyyoyin kasar nan ya nuna a fili an fifita wasu wuraren fiye da wasu, inda jihar Lagos ita kadai ta samu kashi arba’in da bakwai na rabon, yayin da sashen kudu maso kudu ke bi mata da kashi goma sha bakwai cikin dari.

Gwamnan wanda mataimakinsa Aminu Abdul-Salam Gwarzo ya wakilta a taron, ya ce rabon ya nuna rashin adalchi, da kaucewa tanadin kundin tsarin mulkin kasa, saboda haka ba ya bisa ka’ida.

Gwamnan Kano dai ya yi kira ga hukumomin da abun ya shafa, da majalisar dokokin tarayya su daidaita wannan kuskure, tare da tabbatar da ganin an dauki mataki kan wadanda su ka yi wannan rabon kudi maras ma’ana.

Latest stories

Related stories