Saurari premier Radio
21.8 C
Kano
Saturday, March 2, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiShugaba Bola Tinubu na shirin tafiya birnin Nairobi don halartar taron AU

Shugaba Bola Tinubu na shirin tafiya birnin Nairobi don halartar taron AU

Date:

Yanzun haka shugaba Bola Tinubu na shirin tafiya birnin Nairobin Kenya domin halartar taron tsakiyar shekara na gamayyar kungiyoyin hadin kan Afrika, da na rassan kungiyoyin tattalin arzikin kasashen yankin Afirka.

Wata sanarwar kakakin shugaban, Dele Alake, ta ce Tinubu zai bar Abuja yau Asabar domin halartar wannan taro da za a gudanar gobe Lahadi.

A matsayinsa na shugaban kungiyar ECOWAS, Bola Tinubu zai gabatar da rahoton ci gaban da kungiyar ta samu cikin wata shida da suka gabata a fannin kasuwanci, da walwala, da zuba jari, da samar da abubuwan more rayuwa, da zaman lafiya da tsaro tsakanin kasashen yammacin Afrika.

Latest stories

CBN Ya Kwace Lasisin Yan Canji Sama da Dubu Hudu A Faɗin Nijeriya

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da soke lasisin...

Dangote ya bayar da shawarar mayar da kasuwar waya ta Farm Center zuwa cibiyar fasaha

Fitaccen attajirin nan, Alhaji Aliko Dangote, ya shawarci jami'ar...

Related stories