Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiNiMet ta yi hasashen samun mamakon ruwan sama a wasu jihohin.

NiMet ta yi hasashen samun mamakon ruwan sama a wasu jihohin.

Date:

Wani has ashen hukumar Kula da Yanayi ta kasa NiMet ya nuna cewa akwai yiwuwar samun mamakon ruwan sama a wasu jihohin kasar nan Tsakani yau Laraba zuwa ranar Juma’a.

Ana sa ran samun ruwan sama kamar da bakin kwarya daga safiyar yau Laraba a sassan Oyo, Kwara, Osun, Ekiti, Ondo, Kogi, Bayelsa, Ribas, Akwa Ibom, Cross River, Benue, Taraba, Plateau, Niger, Ogun, Kaduna, babban birnin tarayya da jihar Zamfara.

NiMet ta kuma yi hasashen cewa za a samu iska mai karfi a lokacin ruwan saman a sassan Oyo, Kwara, Osun, Ekiti, Ondo, Kogi, Bayelsa, Ribas, Akwa Ibom, Cross River, Benue, Taraba, Plateau, Niger, Ogun, Kaduna, Babban Birnin Tarayya. da jihohin Zamfara.

Latest stories

Related stories