Saurari premier Radio
27.4 C
Kano
Friday, April 26, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAddini2023: Malamai su daina yiwa 'yan siyasa addu'a don neman kudi-Muhammadu Sanusu...

2023: Malamai su daina yiwa ‘yan siyasa addu’a don neman kudi-Muhammadu Sanusu II

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Tsohon Sarkin Kano kuma Halifan Tijjaniyya a Najeriya, Muhammad Sanusi II, ya shawarci malaman addini da su yi a hankali da ‘yan siyasar da za su dinga zuwa wajensu neman addu’a yayin da zaɓukan 2023 ke ƙaratowa.

Halifa Sanusi ya bayyana haka ne a jiya Litinin a Abekuta lokacin da ya kai ziyara ga Babanla Adinni of Egbaland, Chief Tayo Sowunmi.

Ya yi kira ga malamai da su yi wa ‘yan takarar da suka cancanta addu’a, maimakon mayar da addu’ar abar neman kudi.

“A matsayinnu na shugabannin addini, ya kamata mu daina yi wa ‘yan siyasar da suke ba mu kudi addu’a a lokacin zaɓe.

“Kamata ya yi mu duba dukkan ‘yan takarar mu gano waɗanda suka cancanta masu gaskiya mu yi musu addu’a da kanmu”, in ji shi.

Halifa Sanusi ya ce ba shi da burin yin takarar shugaban ƙasa.

Ya ce ya fifita ilimin addini da sarauta da Allah ya ba shi fiye da komai.

Latest stories

Related stories

Kotun umarci a bai wa lauyoyin Murja Kunya dama su rika ganawa da ita

MurjaBabbar Kotun jiha Kano ta umarci a bai wa...

Daurawa ya sauka daga mukaminsa na babban kwamandan Hisbah

Sheikh Daurawa ya sauka daga mukaminsa na babban kwamandan...