Saurari premier Radio
30.9 C
Kano
Tuesday, May 7, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAddiniKotun umarci a bai wa lauyoyin Murja Kunya dama su rika ganawa...

Kotun umarci a bai wa lauyoyin Murja Kunya dama su rika ganawa da ita

Date:

MurjaBabbar Kotun jiha Kano ta umarci a bai wa lauyoyin Murja Kunya dama su rika ganawa da ita.

Inda a yanzu asibitin Nassarawa suka bi umarnin, har ma lauyoyin sun yi ganawar farko da ita.

Sannan kotun ta tsayar da shari’ar da ake yi a kotun Kwana Hudu har sai an gama sabuwar shari’ar.

Idan za’a iya tunawa kotun shari’ar musulunci dake Kwana Hudu a zaman ta na karshe, ta bayar da umarnin kai Murja Kunya, asibitin masu tabin hankali domin duba lafiya ƙwaƙwalwarta.

Wadanda aka yi karar su ne kwamishinan shari’a jihar Kano, alkalin kotun shari’ar Musulunci dake Kwana Hudu, Malam Nura Yusuf Ahmad, kwamishinan yan sandan jihar Kano, hukumar kula da asibitocin jihar Kano, asibitin masu tabin hankali na tarayya dake Dawanau.

Murja a cikin wata takarda da lauyanta ya gabatar, ta roki kotu da ta umarci wadanda ake kara na 4 da na 5, da su bayar da dama a rika ganin ta matukar bukatar hakan ta taso ba tare da wata matsala ba.

Bayan sauraron dukkanin bangarorin biyu, mai shari’a Nasiru Saminu ya amince da bukatar Murja Kunya da lauyanta.

Kotun ta kuma umurci wanda ake kara na 5 wato hukumar kula da asibitin jihar Kano, da ta bai wa lauyan Murja kunya kwafin rahoton lafiyar kwakwalwar da aka yi mata.

Kotun ta dage ci gaba da sauraren karar zuwa ranar 20/03/2024 domin jin asalin sammacin.

Latest stories

Related stories