Saurari premier Radio
35.9 C
Kano
Friday, June 14, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiFursunoni sun gudanar da zanga-zanga a gidan gyaran hali na jihar Filato

Fursunoni sun gudanar da zanga-zanga a gidan gyaran hali na jihar Filato

Date:

Fursunoni a wannan Juma’ar sun gudanar da zanga-zanga a gidan gyaran halin Jos da ke Jihar Filato saboda yunƙurin mahukunta na rage musu kasafin abinci.

Boren da fursunonin ke yi na zuwa ne bayan sun samu labarin cewa akwai tsare-tsaren da hukumar kula da gidajen yari ta yi na fara sassabe kasafi da kuma rage ingancin abincin da ake ba su.

Bayanai sun ce dangane da wannan bayanan sirri da masu zaman waƙafin suka samu ne suka ɗaura ɗamarar ganin ba a yi musu sagegeduwa ba a fannin abincinsu.

Wasu daga cikin martanin da fursunonin suka aiwatar sun haɗa da bijire wa umarnin gandirebobi sabanin yadda suka saba yi musu ladabi a baya, da kuma ƙaurace wa yin karin kumallon safe da kafa dandazo a tsakar gidan zaman ɗan Kanden, lamarin da aka riƙa watsa musu barkonon tsohuwa domin kora su ɗakunansu.

Jaridar Daily Trust ta tuntubi Kwanturolan Gidan Yarin Jos, Raphael Ibinuhi, ya tabbatar da faruwar lamarin.

A cewarsa, matsalar da suke fuskanta a yanzu ita ce farashin kayayyakin abincin sun yi tashin gwauron zabi a kasuwa.

Hakan ya sanya dole za su rage kasafin abincin da ake raba wa fursunoni.

Yace wannan mataki ne ya fusata fursunonin har suke bore.

Latest stories

Related stories