Saurari premier Radio
24.8 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiDangote ya bayar da shawarar mayar da kasuwar waya ta Farm Center...

Dangote ya bayar da shawarar mayar da kasuwar waya ta Farm Center zuwa cibiyar fasaha

Date:

Fitaccen attajirin nan, Alhaji Aliko Dangote, ya shawarci jami’ar Bayero ta hada hannu da gwamnatin Kano wajen sauya fasalin kasuwar waya ta Farm Center zuwa cibiyar fasaha dan bunkasa tattalin arziki.

Alhaji Aliku ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da mukala a bikin yaye dalibai na jami’ar Bayero karo na 38 da ke gudana a harabar jami’ar.

Dangote wanda ya samu wakilcin guda daga cikin na hannun damansa Injiniya Mansur Ahmad ya ce mayar da kasuwar zuwa cibiyar nazari da bunkasa fasahar sadarwa zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin jihar nan.

A cewarsa gwamnati ce za ta taimaka wajen sanya kudade a makarantu domin su dauki gabar inganta kasuwar wajen mayar da ita yadda za ta anfanar da jama’a ta hanyar ilimi.

Haka kuma Alhaji Alikon ya ce cibiyarsa na hadin gwiwa da jami’o’i da kungiyoyi wajen bunkasa ilimin matasa.

Latest stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

Related stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...