Saurari premier Radio
24.2 C
Kano
Monday, September 9, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAddiniDattijuwa mai shekaru 60 ta sauke Al’kur’ani a Kano

Dattijuwa mai shekaru 60 ta sauke Al’kur’ani a Kano

Date:

Ashiru Umar da Shehu Usman Salihu

Wani abu da ba safai aka saba gani a Kano ba shi ne a ga dattijai mata na zuwa makarantun islamiyya har ma su samu damar yin sauka da yara kanana.

Sai dai ya yin da makarantar Nasidi AC Littahfizul Qur’an da ke filin Burji a unguwar Bakin Ruwa da ke karamar hukumar Dala ke bikin yaye daliban da suka sauke, an hango wata dattijuwa mai shekaru 64 cikin daliban da suka yi saukar.

Makarantar dai ta yi bikin yaye dalibai 53 ne da suka sauke Alkur’ani a bana ranar Asabar.

Ita dai wannan dattijuwa Fatima Bello ta fitar da kunya da jin nauyi ta kuma koma karatu tare da jikokinta har kuma ta kammala aka yaye da ita.

Yayin da take zantawa da Premier Redio Fatima ta ce ta yi saukar ne tare da jikanta da suka kamala a aji daya.

“Bayan da mai gidana ya saya min takardar shiga makarantar na fara karatu da ‘ya‘yana da jikoki na.

“Saukar farko aka yi  da ‘yata ta ciki na, ni kuma ina daliba ban sauke ba, sauka ta biyu aka yi da jikata.

“Sai kuma yanzu da aka yi sauka ta hudu muka yi tare da dan autana.

“Tunda na fara zuwa makaranta bana fashin zuwa, ko tafiya zanyi zan lissafa kar ta zo min Asabar da Lahadi, idan biki ne ko suna bana zuwa har sai an tashi daga makaranta,” Fatima ta bayyana.

Ta kuma yi kira ga mata da su fahinci cewa girma ba ya hana karatu, a cewarta neman ilimi haske ne a don hakan ta bukaci mata su dage su nemi ilimi.

A nasa jawabin shugaban makarantar Abdulqadir Balarabe Nasidi ya ce makarantar na bin matakai na koyawa dalibai baki kafin a sanyasu fara karatu.

Ya ce matukar dalibi ya koyi baki to shakka babu da an dorasu akan al’kur’ani to babu yadda za a yi su kasa fitar da abinda ake so.

Ya ce wannan sauka ita ce sauka ta hudu da aka yi aka kuma yaye dalibai sama da dari.

Latest stories

Ni zan yi nasarar lashe zaben shugaban kasa a 2027 – Kwankwaso

"Ni zan yi nasarar lashe zaben shugaban kasa a...

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Ni zan yi nasarar lashe zaben shugaban kasa a 2027 – Kwankwaso

"Ni zan yi nasarar lashe zaben shugaban kasa a...

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...