Saurari premier Radio
39.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiRikicin APC zamu daukaka kara- Dan Zago

Rikicin APC zamu daukaka kara- Dan Zago

Date:

Tsagin Sanata Ibrahim Shekarau a jam’iyyar APC a Jihar Kano da ke rikici da na Gwamna Abdullahi Ganduje ya ce zai ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotu da ya ce shugabancin ɓangaren gwamna ne halastacce.

Shugaban tsagin, Ahmadu Haruna Zago, wanda ke samun goyon bayan tsohon Gwamna Sanata Ibrahim Shekarau, ya faɗa wa BBC Hausa cewa za su yi biyayya ga hukuncin amma za su ɗaukaka ƙara.

“Za mu ɗaukaka ƙara mana, ai bin umarnin daban kuma ɗaukaka ƙara daban,” in ji shi. “Lauyoyinmu na nazari kan hukuncin kotun.”

Hakan na nufin Kotun Ƙoli ce za ta raba gardama idan suka ɗaukaka ƙarar, kasancewar Kotun Ɗaukaka Ƙara ce ta yi hukuncin na yanzu.

A zaman da ta yi yau Alhamis a Abuja, Kotun Ɗaukaka Ƙara ta ce Babbar Kotun Abuja ba ta da hurumin yin hukunci kan rikicin sannan kuma ta ce shugabancin Abdullahi Abbas ne halastacce – ba na Haruna Zago ba.

A makon da ya gabata ne tsagin Shekarau ya yi watsi da wani yunƙurin sulhu da jam’iyyar ta ƙasa ta yi, inda ta naɗa Gwamna Ganduje a matsayin jagoran kwamatin sasanta rikicin da suke yi.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories