Saurari premier Radio
31.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiRikicin APC: Banza bakwai ta shuka dusa -Ganduje

Rikicin APC: Banza bakwai ta shuka dusa -Ganduje

Date:

Jim kadan bayan samun nasarar da tsagin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje yayi a Gaban kotu gwamnan yayi zazzafan martani irin na siyasa.

Gwamna Ganduje yace a yayin da wasu suke shuka iri, wasu sun shuka dusa.

Ya kuma kara da cewa “Banza bakwai ta shuka dusa”

Wannan kalamai na gwamna Ganduje ana ganin zasu bude wani sabon babi na siyasa a jihar Kano a daidai lokacin da ake kokatin yin sulhu tsakanin Tsagin Shekarau da Gandujen.

A yau ne dai kotun daukaka kara tayi watsi da hukuncin kotun da ta tabbatarwa da tsagin Sanata Malam Ibrahim Shekarau nasara, inda kotu tace kotun da tayi hukunci a baya bata da hurumin yin wannan hukunci.

 

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories