Saurari premier Radio
25.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiMatashi ya ginawa kansa kabari na kusan Milyan 2

Matashi ya ginawa kansa kabari na kusan Milyan 2

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Wani bawan Allah mai suna Patrick Kimaro Dan kasar Tanzaniya ya ginawa kansa kabari  na kimanin N 1,700,000 da za a binne shi idan ya mutu.

Mista Kimoro mai shekaru 59 ya gina kabarin ne don ragewa dangi wahalar da ake Sha yayin jana’iza.

Wannan al’amari dai ya tayar da hankalin mutane sosai a Tanzaniya ganin cewa ba kasafai ake samun irin haka ba.

Shugabannin gargajiya a yankin Kilimanjaro, Inda mista Kimoro ya fito sun ce bai kamata a gina ƙabari ba, don jiran mutuwa.

Haka kuma sunce  bai kamata ƙabari ya kasance ba komai a cikinsa ba tsawon lokaci.

Tun Janairu, 2022 ne ya fara gina ƙabarinsa domin rage wa iyalansa ɗawainiyar jana’izarsa idan ya mutu, kamar yadda ya bayyana wa BBC Suwahili.

Ya ce ya yi haka ne don ya sauƙaƙa wa iyalansa ɗawainiyar jana’iza idan ya mutu, duba da shi ma yadda ya sha wahala a lokacin da iyayensa suka rasu.

Mista Kimaro bai tsaya a nan ba domin kuwa yana shirin yi wa kabarin nasa inshora ko da za a samu matsala irin ta ambaliyar ruwa da za ta iya lalata shi.

Latest stories

Related stories