Mukhtar Yahya Usman
Hukumar kididdiga ta kasa NBS ta ce karancin man fetur da ake fama da shi a kasar nan zai kawo hauhawar farashin kayan masarufi.
Shugaban sashen kiddiga na hukumar Dr Simon Harry, ne ya bayyana hakan ya yin da yake zantawa da manema labarai ranar Talata.
Ya ce matukar ba a dauki mataki ba lamarin ka iya tabarbara komai a kasar nan.
Dr Harry ya ce ƙarancin man zai haifar da fargaba kan tattalin arziki ta yadda farashin kayan abinci za su tashi da kuma ladan ayyuka.
“Ko muna so ko ba ma so, masu safarar kaya za su yi amfani da wannan damar wajen Æ™ara kuÉ—in dako,” in ji shi.
Haka kumar ta (NBS) ta ce an samu raguwa a hauhawar farashin kaya a kasar nan a watan Janairun da ya gabata da kashi 0.34 cikin 100 idan aka kwatanta da Disamban 2021.
Yanzu haka dai ana sayar da lita ɗaya ta man fetur ɗin kan N500 ko fiye a Abuja yayin da gidajen mai ƙalilan ne ke sayar da man.
A gefe guda kuma, kamfanin mai na Najeriya, NNPC, ya ce ya bayar da umarnin dakon mai daga manyan rumbuna da kuma sayar da shi a gidajen mai a fadin kasar, ba dare ba rana a kokarin kawo karshen matsalar.
A wata sanarwa da kamfanin ya fitar jiya Talata, NNPC ya ce yana ba wa ‘yan kasar tabbacin daukar matakan da suka dace domin hanzarta samar da man a fadin kasar.