33.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiGanduje ya amince a fitar da Naira Biliyan 1 don biyan garatutin...

Ganduje ya amince a fitar da Naira Biliyan 1 don biyan garatutin ma’aikata

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Mukhtar Yahya Usman

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya amince a fitar da Naira biliyan daya domin biyan kudaden garatutin ma’aikatan da suka yi ritaya.

Gwaman ya bayyana hakan ne ranar Talata lokacin da yake kaddamar da sabuwar sakatariyar kungiyoyin ma’aikatan gwamnati na jihar Kano.

Gwanan wanda ya samu wakilcin shugaban hukumar Fansho ta jiha Alhaji Sani Dawaki Gabasawa, ya ce gwamnati za ta ci gaba da kulawa da walwalar yan fansho a jihar nan.

Ya kuma yabawa kungiyar kan irin rawar da ta taka karkashin shugabanta Hashim Sale.

A nasa jawabin shugaban kungiyar kwadago ta jihar Kano kwamared Kabiru Ado Minjibir godewa gwamnan ya yi da ya amince a fitar da kudaden domin biyan yan fanshon.

Shima da yake jawabi shugaban kungiyar Hashim Sale ya ce sun gina sabuwar sakatariyar ne da kudaden da suke tarawa a tsakaninsu.

Ya kuma godewa daukacin mambobin kungiyar bisa irin hadin gwiwar da suke bashi wajen tafiyar da al’amuran jama’a.

Latest stories