Saurari premier Radio
37.5 C
Kano
Tuesday, June 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKasuwanciKarancin wutar lantarki:KEDCO ya baiwa jama’a hakuri

Karancin wutar lantarki:KEDCO ya baiwa jama’a hakuri

Date:

Aminu Abdullahi Ibrahim

Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kano, KEDCO ya baiwa al’umma a Kano da Jigawa hakuri na karancin wutar lantarki da a ke samu  a ƴan kwanakin nan.

A wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Kamfanin, Ibrahim Sani Shawai ya fitar, ya ce matsalar ta afku ne sakamakon raguwar adadin wutar da kanfanin tunkudu wutar lantarki na kasa TCN ya yi a kwanakin nan

Ya ce ita ma hukumar ta TCN ta fuskanci ƙarancin wutar ne sakamakon ƙarancin wutar da ga Kamfanonin da su ke samar da ita wato ‘Generation Companies’ zuwa ga KEDCO.

Ya ce an fi samun ƙarancin wutar da ga ƙarfe 6 na yamma da kuma 11 na dare.

Bayan da ya baiwa al’umma haƙuri, Shawai ya tabbatar da cewa za a shawo kan lamarin nan ba da daɗewa ba.

Latest stories

Makiyaya sunyi watsi da dokar kafa hukumar kiwo ta ƙasa.

Makiyaya a kasar nan sun yi watsi da kudirin...

Za’a iya shafe shekaru kafin kawo ƙarshen ƴan bindiga”- Sarkin Musulmi.

Mai Alfarma Sarkin Muslmi, Sultan Sa’ad Abubakar III, ya...

Related stories