Saurari premier Radio
37.9 C
Kano
Sunday, May 5, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin tarayyaGwamnatin tarayya ta fara wani yunkurin karya farashin makamashin Gas na girki...

Gwamnatin tarayya ta fara wani yunkurin karya farashin makamashin Gas na girki a kasar nan

Date:

Gwamnatin tarayya ta fara wani yunkurin karya farashin makamashin Gas na girki a kasar nan bayan kafa wani kwamiti da aka dorawa alhakin lalubo hanyoyin wadata gas din a ko’ina, da nufin karya farashinsa nan da mako daya.

Wata sanarwar Lousi Ibah, kakakin karamin ministan man fetur Ekperikpe Ekpo, ta ce gwamnati ta damu kwarai game da yadda farashin Gas din yayi tashin gwauron-zabo, daga naira dari bakwai zuwa dubu da dari daya kilo guda.

Sanrawar ta kara da cewa, tuni ministan ya gana da wakilan kamfanonin mai na Chevron da NNPC a Abuja, inda aka tattauna yadda za a shawo kan matsalar.

Cikin manyan matsalolin da aka ce suna haddasa tashin farashin Gas din dai sun hada har da karancinsa, da rashin samun musayar dala cikin sauki ga ‘yan kasuwar dake shigo da shi kasar nan.

Sanarwar Ministan ta kara da cewa, duk kasar da ta damu da al’ummar ta to bukatarsu ce kan gaba har kullum, saboda haka gwamnati zata tabbatar da ganin farashin gas din ya karye daidai, lokacin da ake tunkarar bukukuwan kirsimeti da na sabuwar shekara.

Latest stories

Sarkin musulmi ya ja hankalin shugabanni kan samarwa da al’umma makoma

Mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na 3...

Related stories

Sarkin musulmi ya ja hankalin shugabanni kan samarwa da al’umma makoma

Mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na 3...