Saurari premier Radio
33.9 C
Kano
Saturday, May 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin tarayyaShugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya isa zauren majalisar dokokin domin gabatar...

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya isa zauren majalisar dokokin domin gabatar da kasafin kudi.

Date:

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya isa zauren majalisar dokokin ƙasar domin gabatar da kasafin kudinsa na farko a matsayin shugaban kasa.

Tinubu wanda ya isa da misalin karfe 11 na safe tare da rakiyar wasu Ministoci da manyan mataimaka.

Kudirin kasafin kudi na Naira Tiriliyan 27.5 shi ne na farko da Shugaba Tinubu zai gabatar tun bayan hawansa mulki a ranar 29 ga Mayu.

Haɗakar majalisar dattawa da ta wakilai ne shugaba Tinubun zai gabatar wa kasafin kuɗin.

Shugaban ya ce akwai buƙatar ‘yan majalisar dokokin ƙasar su riƙa tsefe kasafin kuɗin ƙasar kafin su amince da shi.

Tinubu ya ce hakan zai bayar da dama ga gwamnati wajen cika alƙawuran da ta ɗaukar wa ‘yan ƙasar a lokacin yaƙin neman zaɓe.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...