Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Thursday, February 22, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiAn shiga rudani dangane da hukuncin kotun daukaka kara game da zaben...

An shiga rudani dangane da hukuncin kotun daukaka kara game da zaben gwamnan Kano

Date:

An shiga rudani dangane da hukuncin kotun daukaka kara game da zaben gwamnan Kano tsakanin Abba Kabir Yusuf da Nasiru Gawuna, bayan da wata takarda daga kotun ta nuna ta kori karar, tare da jingine hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe a gefe.

Kotun ta kuma umarci wanda ake kara ya biya tarar naira milyan daya ga wanda ya daukaka kara.

Takardar dauke da sa hannun Alkalin kotun daukaka kara Moore Asiemo, ta zayyano wadannan bayanai masu sarkakiya.

Sai dai Barista Zurkallaini Sani Tsanyawa, wani masanin sharia ya ce idan kuskure kotun daukaka kara tayi ko kuma wata hikima ce ta daban, to kotun koli za ta gyara komai.

Wanann ta sa wakilinmu Faisal Abdullahi Bila ya tuntubi Barista Zurkallaini Sani Tsanyawa domin neman warware abun da ya fahimta game da takardar shariar.

Barista Zurkallaini Tsanyawa ya kuma ce idan kuskure kotun ta yi, ko kuma wata hikima ce ta daban, to babu makawa kotun koli za ta gyara komai.

Latest stories

Related stories