Saurari premier Radio
25.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiJam’iyyar NNPP ta amsa tayin tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar na...

Jam’iyyar NNPP ta amsa tayin tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar na hadewa wuri guda

Date:

Jam’iyyar NNPP ta amsa tayin tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar na hadewa wuri guda domin tunkarar APC a zaben dake tafe nan gaba.
Mukaddashin shugaban NNPP ta kasa, Abba Ali, ya yi maraba da kiran Alhaji Atiku na dunkulewa guri guda.

Sai dai jamiin hulda da jamaa na jamiyyar NNPP a nan Kano, Musa Nuhu ‘Yankaba, ya ce duk da jamiyyarsa na goyon bayan hadakar, hakan ba ya nufin za su marawa Alhaji Atiku baya a zaben shugaban kasa mai zuwa.

Musa ‘Yankaba ya kara da cewa, za a iya kwace mulki a hannun APC idan aka dunkule wuri guda kamar yadda Rabiu Musa Kwankwaso ya jagoranci kawar da PDP da ta shafe shekaru ta na mulkin kasar nan.

Alhaji Atiku Abubakar da shi ne dan takarar jamiyyar PDP a zaben shugaban kasa da ya gabata, ya jima yana neman hadewa da NNPP da Labour Party a wani yunkuri na tankwabe mulki daga jam’iyyar APC, amma jamiyyun biyu na ta biris da shi domin su na ganin ba za su marawa Atiku baya ya shugabancin kasar nan ba.

Latest stories

Related stories