24.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeAl'aduAyi Yakin Neman Zabe Cikin Lumana- Sarkin Bichi

Ayi Yakin Neman Zabe Cikin Lumana- Sarkin Bichi

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

ABDURRASHID HUSSAIN

Mai Martaba Sarki Bichi Alh. Nasir Ado Bayero yayi kira ga yan takarkaru a zabe mai zuwa da su yi yakin neman zabe cikin lumana da kwanciyar hankali domin samun cikakken hadikan yan kasa.

Sarkin yayi kiran ne a fadarsa lokacin da ya karbi bakuncin kungiyar “THE ASIWAJU GROUP” karkashin jagorancin Alh. Abdulrazak Dan’Azumi.

Alh. Nasiru Ado Bayero ya kuma yi kira da su sa cigaban kasa gaba wajen yin dukkan ayyukansu.

A jawabinsa shugaban kungiyar na kasa Alh. Abdulrazak Dan’azumi, yace sunje fadar sarkin ne domin neman albarkarsa.

Hakan kuma mai martaba sarki na Bichi ya nada Alh. Ahmad Tatsan a matsayi sabon dagacin garin Tatsan dake karamar hukumar Tsanyawa.

Bayan nadin kuma sarkin ya hori sabon dagacin, da ya zama mai sulhu ga talakawansa tare hadakai ga jami’an lafiya domin yaki da cutuka.

A jawabinsa sabon dagacin Alh. Ahmad Tatsan ya godewa Allah bisa nadin, tare da alkawarin yin aiki takuru domin cigaban talakawansa.

 

Latest stories