25.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiSiyasaKwankwaso Yaci Amanar mu- Shekarau

Kwankwaso Yaci Amanar mu- Shekarau

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

ABDULRASHID HUSSAIN

Sanata Kano ta tsakiya Malam Ibrahim Shekarau, ya ce dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP Rabiu Musa, ya ci amanar shi da mabiyansa, inda ya bayyana hakan a matsayin dalilin da ya sa suka fice daga jam’iyyar.

 

Ya bayyana haka ne a wata hira da gidan talabijin na Channels.

 

Yace da gangan jagoran Kwankwasiyyar ya jinkirta aiwatar da yarjejeniyar da suka cimma kafin ya koma jam’iyyar har zuwa lokacin da hukumar zabe ta kasa INEC ta rufe karbar yan takara.

 

Shekarau ya kara da cewa ya yi mamakin ganin jerin sunayen yan takarar da aka rubuta da hannu da shugabannin jam’iyyar NNPP suka fitar a nan Kano.

Latest stories