25.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiGwamnatin KanoGanduje Ya Maye Gurbin Kwamishinonin da Sukayi Murabus Domin Tsayawa Takara

Ganduje Ya Maye Gurbin Kwamishinonin da Sukayi Murabus Domin Tsayawa Takara

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Gwamnatin Kano ta rantsar da sabbin kwamishinoni 11 d zasu maye guraben wadanda suka yi murabus domin tsayawa takara.

 

Wannan na zuwa ne a wani taro na musamman da aka shirya karkashin jagorancin gwamna Abdullahi Umar Ganduje, da ya gudana a dakin taro na filin wasa na Sani Abacha dake Kofar Mata.

 

Ganduje ya bayyana kwarin gwiwar cewa wadanda ya nada nada kwarewar aiki da kuma kishin jihar Kano, inda yace tabbas zasu gayar da gudun mawa wajen ciyar da al’ummar jihar gaba.

 

Cikin wadanda aka rantsar din akwai Dr. Jibril Yusuf rurum – Ma’aikatar Noma, Ya’u Abdullahi Yan Shana – Ma’aikatar Ilimi, Alhaji Ibrahim Dan azumi Gwarzo – Ma’aikatar kasafi da tsare-tsare, Abdulhalim Abdullahi Liman – ma’aikatar Raya karkara, Alh. Lamin Sani Zawiyya – Ma’aikatar kananan Hukumomin da Masarautu, Hon. Garba Yusuf Abubakar – ma’aikatar Ruwa, Hon. Adamu Abdu Panda – ma’aikatar kudi da cigaban tattalin arziki, Hon. Sale Kausani – ma’aikatar gidaje da sufuri, Alh. Ali Musa Hamza Burum-burum – Ma’aikatar kula da yawun bude idanu da al’adun, Dr. Aminu Ibrahim tsanyawa – Ma’aikatar Lafiya, da kuma Alhaji Kabiru Muhammad – Ma’aikatar Aiyuka na Musamman.

Latest stories