Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Friday, February 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAtiku zai karbi Shekarau a Kano

Atiku zai karbi Shekarau a Kano

Date:

Mukhtar Yahya Usman

 

A yau Lahadi ake sa ranar Alhaji Atiku Abubakar, zai ziyarci Kano domin karbar Malam Ibrahim Shekarau, zuwa jam’iyyar PDP.

 

Ana sa ran Atiku Abubakar zai sauka a filin jirgin Saman Malam Aminu Kano da misalin karfe 5:00 na yammacin Lahadin nan.

 

Haka kuma ana sa ran dubban masoya daga jam’iyyar PDP za su yi dafifi zuwa wajen tarar tasa, inda ake sa ran gudanar da al’amuran siyasa da dama.

 

Idan za a iya tunawa tun a shekarar 2019 ne Malam Ibrahim Shekarar ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC inda aka zabe shi sanatan Kano ta tsakiya.

 

Sai dai ya fice daga jam’iyyar zuwa NNPP ne bayan da aka samu takun saka tsakaninsa da gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje.

 

Watanni kadan bayan shigarsa jam’iyyar ta NNPP kuma ya zargi anyi masa ba dai-dai ba har ma yake yunkurin ficewa.

 

NNPP jam’iyyar zalunci

 

A wani taron manema labarai da Malam Ibrahim Shekarau ya gudanar a baya bayan nan an jiyo shi yana wasu maganganu a fusace.

 

Shekarau ya zargin tsohon gwamnan Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da ‘yaudara da zalunci da kuma cin mutunci’.

 

“Da mu zauna cikin rashin mutunci da yaudara da zalunci gwara idan siyasar ce ma mu daina.” A cewarsa.

 

Manyan jam’iyyu na zawarci na

 

Malam Ibrahim Shekarau ya ce ‘yan takarar shugaban kasa a manyan jam’iyyu na zawarcinsa dan ya yi musu takarar mataimakin shugaban kasa.

 

Ya ce da yawa sun nemeshi don ya yi mataimakin shugaban kasa amma da yake ba kudi yake nemaba hakan ta sa ya watsar da su.

 

“Manyan ‘yan takarar nan sun neme ni na yi musu takarar mataimaki amma na ki, saboda ba kudi nake nemaba”

 

Bani da matsala da Shekarau

 

Sai dai a wata tattaunawa da ya yi da sashin Hausa na BBC Sanata Rabi’u Kwankwaso ya ce ba shi da wata matsala da Shekarau da za ta sa ya fusata.

 

Kwankwaso ya ce korafin da suke yi na cewar an hana su kujeru ko kuma wasu mukamai ba gaskiya ba ne.

 

A cewarsa, Shekarau ya shiga jam’iyyar ne bayan an gama rabon dukkanin mukamai kuma lokaci ya kure ba za a iya canzawa daga hukumar INEC ba.

 

Adon hakan ne ma ya roki Shekarau din da ya hakura ya zauna a ci gaba da tafiya tare.

 

Muna maraba da Shekaru

 

A nata bangaren jam’iyyar PDP a Kano ta ce tana maraba da shigar Malam Shekarsu cikinta.

 

Shugaban Jam’iyyar a Kano Shehu Wada Sagagi ne ya yi maraba da shigar tasa cikin jam’iyyar.

Sagagi ya ce sun ji dadi kwarai da batun shigar malam Shekarau jam’iyyar, domin kuwa a yanzu jam’iyyar ta samu jagora a Kano.

 

Sagagi ya ce duk da rigingimun da ke cikin jam’iyyar ta PDP sun yarda su zubda makamansu su bi Malam Ibrahim Shekarau.

 

A halin yanzu dai akwai rigingimu a jam’iyyar PDPn Kano, inda har yanzu ake kai ruwa rana tsakanin tsagin Sadiq Wali da Bello Hayatu Gwarzo ke jagoranta, da kuma Muhammad Sani Abacha da Shehu Wada Sagagi ke jagoranta.

 

Dukkan bangarorin biyu suna da ‘yan takara masu kama da juna a mukaman siyasa iri daya.

Latest stories

Related stories