Shehu Usman Salihu
Ɗan takarar gwamnan jihar Kano a jam’iyyar ADP, Sha’aban Ibrahim Sharada, ya naɗa Abbas Yusha’u Yusuf a matsayin kakakin kwamitin yaƙin neman zaɓen sa.
Sha’aban Sharada ya amince da nadin nada ne a ranar Lahadi yayin da yake ganawa da manema labarai.
Ya ce sunyi la’akari da irin gogewar da ya ke da ita a harkar aikin jarida na tsawon lokaci, kafin nadin nasa.
Ya buƙace shi da ya yi aikinsa bisa tanadin doka da kyautata hulɗa tsakaninsa da abokanan aikin jarida, domin samun kyakkyawan sakamako mai kyau.
Kafin naɗin nasa, Abbas Yusha’u Yusuf shi ne mataimakin sakataren ƙungiyar ƴan jaridu masu ayyukan su a shafukan intanet reshen jihar Kano.
Haka kuma shi mawallafin jaridar Nigerian Tracker dake wallafa labarai a shafin intanet.
Abbas ya yi karatun digirinsa na ɗaya da na biyu akan harkar aikin jarida da sadarwa a jami’ar Bayero.
Haka kuma ya yi aiki da Freedom radio a matsayin wakilinta a gidan gwamnatin Jihar Kano tsawon lokaci kafin ya zama edita, daga bisani ya bar aiki.
Haka zalika sabon Kakakin ya yi aiki a kafafen yaɗa labarai da su ka haɗa da gidan rediyon Rahama da rukunin gidajen rediyon Vision a matsayin Edita.