Saurari premier Radio
28.9 C
Kano
Monday, May 6, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAn zabi na hannun daman Donald Trump a matsayin shugaban majalisar wakilan...

An zabi na hannun daman Donald Trump a matsayin shugaban majalisar wakilan Amurka

Date:

An zabi Kevin McCarthy, a matsayin sabon shugaban majalisar wakilai ta Amurka.

 

An zabi shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai ta amurka Kevin Owen McCarthy, a matsayin sabon shugaban majalisar wakilan a zaben da ‘yan majalisar suka kammala a safiyar Asabar din nan.

 

INEC ta sanar da ranar raba katunan zabe a fadin kasar

 

Zaben nasa ya biyo bayan rashin samun rinjaye da jami’iyar Democrat ta tsohuwar shugabar majalisar Nancy Pelosy, tayi a zaben majalisar wakilan da akayi a baya, wanda hakan yakai ga saukar ta.

 

Kafin zabar sa dai Kevin McCarthy, dan jam’iyar Republican, ya kasance shugaban masu rinjaye na majalisar tun daga shekarar 2019.

 

 

A yanzu dai jam’iyar Republican ta tsohon shugaban Amurka Donald Trump ita ke da rinjaye a majalisar wakilan Amurkan da ‘yan majalisa 222, yayin da jam’iyar Democrat ta shugaba Jeo Biden maici a yanzu keda ‘yan majalisa 212.

Latest stories

Sarkin musulmi ya ja hankalin shugabanni kan samarwa da al’umma makoma

Mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na 3...

Related stories

Sarkin musulmi ya ja hankalin shugabanni kan samarwa da al’umma makoma

Mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na 3...