Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Friday, February 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiINEC ta sanar da ranar raba katunan zabe a fadin kasar

INEC ta sanar da ranar raba katunan zabe a fadin kasar

Date:

Hafsat Nasir Umar

 

Hukumar Zabe mai zaman kanta ta sanar da ranakun da za ta rabar da katinan zabe a fadin kasar.

 

A wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na Tuwita ta ce ta saka ranakun Litinin 12 ga watan Disamba zuwa Lahadi 22 ga watan Janairun 2023 a matsayin ranakun da za ta rabar da katinan zaben a ofisoshinta da ke fadin kananan hukumomin kasar 774.

 

Tuni dai hukumar ta sanar da ranar 25 ga watan Fabrairun 2023 a matsayin ranar da za ta gudanar da zaben shugaban kasar tare da na ‘yan majalisun dokoki.

 

Yayin da za a gudanar da zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi ranar 11 ga watan Maris din 2023.

Latest stories

Related stories