Saurari premier Radio
39.9 C
Kano
Friday, April 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKasuwanciNajeriya zata fara karbar haraji a hannu 'yan crypto

Najeriya zata fara karbar haraji a hannu ‘yan crypto

Date:

Abdulrashid Hussain

 

Najeriya za ta fara karbar haraji daga masu amfani da kundin Internet na crypto currency.

 

Ministar kudi, kasafi da tsare-tsare, Zainab Ahmad, ta sanar da shirin gwamnati na sanya haraji kan kudaden internet na crypto currency da sauran hada-hadar kudi a cikin kudirin sake fasalin dokokin kudi na 2023.

 

Ministar ta bayyana haka ne yayin taron majalisar tattalin arziki ta tarayya da mataimakin shugaban kasa farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranta.

 

A wata sanarwa da mai magana da yawun mataimakin shugaban kasa Laolu Akande ya fitar, yace ministar kudin ta bayyanawa majalisar abunda kudirin karbar harajin ya kunsa.

 

Tace tsarin dokokin da ake son gabatarwa zasu samar da ayyukan yi, habakar tattalin arziki, da kuma sake fasalin yadda ake samun kudin shiga da yadda ake tassarufi da su.

 

Wannan dai na zuwa ne bayan shafe sama da shekara daya da matakin gwamnatin tarayya na haramta kasuwanci kudin internet din na crypto currency.

 

Abunda yasa masu gudanar da hada-hadar kudin internet din suka bayyana karbar harajin daga garesu a matsayin alamun za’a maido da hallacin kasuwancin nasa.

Latest stories

NPFL: Gwamnatin Kano ta bawa Kano Pillars wasa Uku domin ta yi Nasara

Gwamnatin Jihar Kano ta bawa kungiyar Kwallon kafa ta...

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...

Related stories

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...

Farashin Dizel ya koma 1000 a Najeriya

Rahotanni sun bayyana matatar mai ta Dangote ta sanar...