Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Thursday, April 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabarai"Gazawarka ce ta jefa kasar nan cikin mawuyacin hali" Martanin Gwamnoni ga...

“Gazawarka ce ta jefa kasar nan cikin mawuyacin hali” Martanin Gwamnoni ga Buhari

Date:

Gwamnonin jihohin kasar nan 36 sun  zargi gwamnatin Tarayya da jefa Yan Najeriya cikin tsananin matsin rayuwa.

 

Gwamnonin sun kuma zargi Shugaba Buhari da gazawa wajen inganta rayuwar al’ummar kasar nan kamar yanda ya alkawaranta yayin yakin neman zabensa a shekarar 2019.

 

Wannan na kunshe cikin zazzafan martanin da Gwamnonin suka mayar bisa zargin da Shugaba Buhari yayi cewar gwamnonin na satar kudaden kananan hukumomi.

 

Idan za’a iya tunawa Shima Karamin ministan kasafin kudi da tsare-tsare na kasa, Clement Agba, ya zargi gwamnonin jahohi da laifin kididdigar talauci a kasar, yana mai cewa gwamnonin sun yi watsi da kashi 72 cikin 100 na talakawan Najeriya a yankunan karkara, saide suyita gina filayen jiragen sama da gada.

 

Da yake mayar da martani kan wannan zargi a ranar Asabar, Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF), Abdulrazak Bello-Barkindo ya ce  “bai kamata gwamnatin tarayya ta zargi gwamnonin da gazawarta wajen fitar da ‘yan Najeriya daga kangin talauci, samar da tsaro hadi da kyautata rayuwar alumma ba”.

 

“Da farko dai babban aikin kowace gwamnati shi ne tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a. Amma gwamnatin tarayya da ke da alhakin tsaron rayuka da dukiyoyin ta yadda ta bar ‘yan fashi, ‘yan tayar da kayar baya, da masu garkuwa da mutane su mayar da kasar nan filin kisa da nakasa alumma hadi da sace mutane, daga makarantu, kasuwanni,da ma a gonakinsu.

 

“Saboda haka a ra’ayin gwamnoni wannan gazawar da Ministan ke magana a kai, gwamnatin tarayya da yake wakilta ce sanadin jefa kasar a cikin wannan yanayin.”

 

Wani bangare na sanarwar ya kara da cewa, “Gwamnatin tarayya ce, a sakon yakin neman zabenta a 2019, ta yi alkawarin fitar da ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga kangin talauci. A yau bayanai sun nuna cewa sama da ‘yan Najeriya miliyan 130 ne ke rayuwa kasa da tsarin talauci da duniya ta amince da shi na dala daya a rana. A karkashin gwamnatin mai ci da Mista Clement Agba ke rike da mukamin minista, kamfanin NNPC, ya gaza mika kason da doka ta kayyade ga jihohi cikin watanni da dama”

 

“Lamarin da ya tilasta wa gwamnoni dogaro da wasu hanyoyin samun kudaden shiga kamar; shirin SFTAS da sauran ayyukan da NGF ta kafa, don samar da ayyukan jihohi” a cewar sanarwar.

Latest stories

Hukumar EFCC ta musalta zargin da ake mata na fara bincikar tsohon Gwamnan kogi.

Shugaban hukumar EFCC mai hukunta masu yiwa tattalin arziki...

Majalisar dokokin Kano ta nemi a dakatar da KEDCO kan yanke wuta.

Majalisar Dokokin jihar Kano ta bukaci gwamnatin jihar data...

Related stories

Hukumar EFCC ta musalta zargin da ake mata na fara bincikar tsohon Gwamnan kogi.

Shugaban hukumar EFCC mai hukunta masu yiwa tattalin arziki...

Majalisar dokokin Kano ta nemi a dakatar da KEDCO kan yanke wuta.

Majalisar Dokokin jihar Kano ta bukaci gwamnatin jihar data...