Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Friday, February 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiMajalisar Dattawa Za Ta Ji Ra'ayin Jama'a Kan Kafa Sabbin Jami'oi A...

Majalisar Dattawa Za Ta Ji Ra’ayin Jama’a Kan Kafa Sabbin Jami’oi A Dambatta Da Bichi.

Date:

 

Majalisar dattawa ta shirya taron jin ra’ayin jama’a kan kudurin mayar kwalejin aikin gona ta Audu da ke garin Dambatta zuwa cikakkiyar jami’ar aikin gona da kuma mayar kwalejin ilimin fasaha ta Bichi zuwa jami’ar ilimin fasaha duka a nan Kano.

Taron jin ra’ayin wanda kwamitin ilimi mai zurfi na majalisar ya shirya, zai gudana ne a ranar Alhamis 8 ga watan December 2023, a sabon ginin majalisar da ke babban birnin tarayya Abuja.

Don hakan shugaban kwamitin, wakilin Kano ta Arewa, Sanata Barau Jinbrin ke gayyatar dukkan masu ruwa da tsaki zuwa taron jin ra’ayin.

Da yake wa wakilinmu Abdulrasheed Hussain karin bayani, mataimaki na musamman ga sanata Barau Jibrin, Ado Rabi’u Dan Bayero, yace samar da jami’ar a garin Dambatta na cikin kudurori goma da suka gabatarwa sanatan.

Ado Dan Bayero ya kuma bayyana irin ribar da al’ummar garin Dambatta za su samu idan aka samar da jami’ar.

Ya kuma godewa dukkan jagororin yankin kan kokarin da suke na ganin an tabbatar da samuwar wannan jami’a.

Latest stories

Related stories