Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Friday, February 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiShugaba Buhari zai taya Bola Tinubu yakin neman zabe

Shugaba Buhari zai taya Bola Tinubu yakin neman zabe

Date:

Aminu Abdullahi Ibrahim

 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai halarci yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyar APC Bola Ahmad Tinubu a jihohi goma na kasar nan.

 

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai na kwamitin yakin neman zaben Tinubu da Kashim Shettima, kuma ministan ayyuka Festus Keyamo, ya fitar a jiya Juma’a.

 

Ya ce Buhari ya amince da halartar yakin neman zaben Bola Ahmad Tinubu, da za ayi a jihohi goma na kasar nan da suka hada da Yobe da Sokoto da Adamawa da dai sauransu.

 

A watan Nuwambar bara ne dai shugaba Buhari ya halarci yakin neman zaben Bola Ahmad Tinubu da akayi a Jos dake jihar Plateau, bayan ya amince ya zama shugaban kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyar APC.

Latest stories

Related stories